Qassam ta sanar da cewa, Mujahidan wannan bataliyar, sun kai hari da wasu bama-bamai guda uku masu karfin gaske a yammacin Larabar da ta gabata a yankin "Qayzan al-Najjar" da ke kudu da Khan Yunus a kudancin zirin Gaza, kan wasu motocin buldozar Isra'ila guda biyu nau'in D9.
Wannan harin kwanton bauna ga yan mamaya a Khan Yunis yayi sanadiyar kashe wasu da dama daga cikin yahudawan sahyoniyawa da kuma jikkata wasu da dama.
Dakarun Qassam, reshen soji na kungiyar Hamas, sun sanar da cewa mayakansu sun yi wa wani gungun sojojin mamaya na Isra'ila kwanton bauna a yankin "Qayzan al-Najjar" da ke kudancin birnin Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza a yammacin Laraba.
Mujahidan Qassam dai sun janyo wasu gungun sojojin mamaya na Isra'ila zuwa mashigar wani rami da suka dasa bama-bamai. Da isar wadannan dakaru wasunsu kuma suka shiga kofar ramin, sun tayar da bama-bamai da dama, tare da kashe dukkan wadannan dakarun.
Your Comment